An gudanar da bikin buɗe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta nakasassu ta shekarar 2022 ta Beijing

Daga CRI HAUSA

Da yammacin yau ne, aka yi bikin buɗe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta nakasassu ta Beijing na shekarar 2022 a filin wasa na ƙasa da ƙasa dake birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin. Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya sanar da buɗe gasar.

Bikin wanda Zhang Yimou ya jagoranta, yana da taken “Blossoming of Life” an kuma kasa shi zuwa gida 12. Daga cikin masu shirya bikin su 800, kashi 30 cikin 100 mutane ne masu nakasa, kuma an yi haka ne don nuna haɗin kai a cikin al’umma.

Gasar wasannin Olympics ajin nakasassu na lokacin sanyi na Beijing, za ta gudana har zuwa ranar 13 ga Maris, tare da ‘yan wasa na ƙasa da ƙasa da za su fafata a wasanni 78 a manyan wasanni har guda 6, waɗanda suka haɗa da wasan zamiya, da wasan zamiya na yada ƙanin wani, biathlon, snow boarding, da wasan ƙwallon gora na ƙanƙara na nakasassu, da curling na keken guragu.

Fassarawa: Ibrahim