An gudanar da dandalin cibiyoyin ilimi na Sin da Afirka na shekarar 2022

Daga CMG HAUSA

A baya-bayan nan ne aka gudanar da dandalin masu ruwa da tsaki a fannin raya ilimi na Sin da Afirka na shekarar 2022 ta kafar bidiyo, taron da ya hallara wakilai sama da 1400 daga cibiyoyin ilimi na Sin da na ƙasashen Afirka, ciki har da malamai, da dalibai daga manyan jami’o’in Sin, Najeriya, da Habasha da sauran su.

Yayin taron na yini 2, masana da ƙwararru mahalarta, sun yi musayar ra’ayoyi ƙarƙashin jigon “Aiki tare don hangen nesa a fannin raya ilimin malanta, da ingiza burin samar da al’umma guda mai makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka “.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, babban sakataren kwamitin kula da harkokin hukumar UNESCO na ƙasar Sin Qin Changwei, ya ce bisa ga buƙatun ƙasashen Afirka a fannin raya ilimi, Sin tana raba dabarun ta na ci gaban ilimi da ƙasashen nahiyar, kana tana tallafawa ƙasashen na Afirka wajen samar da ƙwararru a dukkanin sassa, kuma tana ingiza bunƙasar harkokin ilimi a nahiyar.

Fassarawar Saminu