An gudanar da taro kan take haƙƙoƙin mutanen asalin Amurka da Kanada da Australia

Daga CMG HAUSA

Yayin zama na 49 na majalisar kare haƙƙoƙin bil adama ta MDD a Geneva, ƙasashen Sin da Venezuela, sun gudanar da wani taron bidiyon mai taken “Yadda Amurka da Canada da Australia suke take haƙƙin mutanen asalin ƙasashen”.

Taron da ya gudana ta kafar intanet, ya samu halartar mutane sama da 150, ciki har da jami’an diflomasiyya dake Geneva da wakilan ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da masana da ‘yan jarida.

Minista Jiang Duan na zaunannen ofishin ƙasar Sin a MDD dake Geneva, ya gabatar rahoto mai taken “hakikanin tarihi da shaidun kisan kiyashin da Amurka ta yi wa Indiyawa” wanda ma’aikatar harkokin wajen Sin ta wallafa a baya-bayan nan, inda ya bayyana cewa, a yanzu mutanen asali na fuskantar wariya a ƙasashen Amurka da Canada da Australia. Yana mai cewa, ya kamata ƙasashen su yi duba kan kurakuran da suka tafka tare da bincike da hukunta waɗanda ke da hannu cikin laifukan take haƙƙoƙin mutanen.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha