An gudanar da taron kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya

Daga CMG HAUSA

An gudanar da taro karo na 7 na kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da fasahohi, a jiya Juma’a.

Kwamitin ya gudanar da taron ne ta kafar bidiyo ƙarƙashin jagorancin mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Qian Keming da ministar kuɗi da tsare-tsare ta Nijeriya, Zainab Ahmed. Jakadan ƙasar Sin Cui Jianchun da mambobin kwamitin daga ƙasashen biyu ne suka halarci taron ta kafar intanet.

Ƙasashen biyu sun waiwayi kyawawan nasarori da suka cimma a haɗin gwiwarsu da ya shafi ciniki da zuba jari da ababen more rayuwa, inda kuma suka yi musayar ra’ayi a kan ƙara inganta hadin gwiwarsu ta fannin tattalin arziki da ciniki.

Haka kuma, a shirye ɓangarorin biyu suke su zurfafa haɗin gwiwarsu, musamman ta fannin manyan ayyuka 9 da aka cimma yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna haɗin gwiwar Sin da Afrika da kuma muhimman ɓangarori 9 na Nijeriya, tare da ci gaba da kyautata walwalar jama’ar ƙasashen biyu da raya dangantakarsu ta tattalin arziki da ciniki cikin aminci.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha