Daga RABI’U SANUSI
Shugaban Ƙaramar hukumar Tarauni Hon Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya jagoranci shirya taron sauraron jin ra’ayin jama’a na yini guda a ƙaramar hukumar Tarauni domin tattauna batun kasafin kuɗin shekara ta 2025 tare da masu ruwa da tsaki.
Taron ya tattaro mambobin al’umma, ƙungiyoyi masu zaman kansu (CBOs), shugabannin ƙaramar hukumar da al’ummar da ke ƙauyuka, limamai, dagatai, masu unguwani da wakilai daga jam’iyyun siyasa don ƙarfafa gaskiya da shirya kasafi bisa buƙatun al’umma.
Hon. Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure ya jaddada muhimmancin hada masu ruwa da tsaki a cikin tsarin kasafi domin tabbatar da cewa kasafin kuɗin 2025 ya dace da buƙatu da muradun al’ummar Tarauni. Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa da ayyukan ci gaba da ya gudanar a yankin wanda ke ƙara inganta cigaban ƙaramar hukumar Tarauni.
Da yake jawabi Kwamishinan Ƙananan hukumomi, Aminu Abdulsalam, Wanda ya sami wakilcin daraktan tsare-tsare na ma’aikatar Ƙananan hukumomi Lirwanu Yusuf ya jinjina tsarin taron tare da bayyana shi a matsayin dandalin buɗe ido ga masu ruwa da tsaki domin su fahimci yadda ake raba kuɗaɗe da shirye-shiryen kashe kuɗin shekara mai zuwa.
Ya nuna jajircewar majalisar kan daidaita kasafin kuɗin da buƙatun al’umma tare da gayyatar mahalarta taron su bayyana damuwarsu, shawarwari da hanyoyin da za a inganta gudanar da gwamnati da isar da ayyuka ga al’umma a yankin.
Daraktan mulki na yankin Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu da shugaban sashen tsare-tsare, bincike da Ƙididdiga Hajiya Binta Ahmed Darma da ma’ajjin ƙaramar hukumar Mallam Bello Hassan sun nuna cikakken goyon bayan wannan gwamnati ga gaskiya da adalci tare da jaddada muhimmancin haɗin kai a cikin tsare-tsare da tsara kasafin kuɗi na kowacce shekara.
Taron tattaunawar ya mayar da hankali ne kan muhimman ɓangarori kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗi, wanda aka yi nufin samar da ci gaban da zai amfani kowa da kowa. Shugabannin ƙauyuka, shugabannin addini da sauran mahalarta sun yi farin ciki da wannan tsarin karɓar ra’ayoyi, inda suka nuna cikakken goyon bayansu ga ayyukan ƙaramar hukumar.
Hakimin yankin ƙaramar hukumar Tarauni sarkin fadar Kano Mallam Ado Kurawa, wanda sakataren sa Jamilu Wada ya wakilta, ya bayyana ƙudirin masarautar na ci gaba da ƙoƙari kan bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa ilimi da inganta ababen more rayuwa a faɗin Ƙaramar hukumar Tarauni.