Daga DAUDA USMAN a Legas
Majalisar fadar Mai martaba Sarkin Guragun Jihar Legas ƙarƙashin jagorancin, Alhaji Amadu Abubakar Gaya, wanda kuma shine Shugaban Majalisar Sarakunan Guragun Legas sun gudanar ta taron yi wa Nijeriya addu’ar ƙarin zaman lafiya da yalwar arziki.
Mahalarta taron sun haɗa da manyan malaman addinin Musulunci na Jihar Legas da sarakunan Guragu na jnguwanni daban-daban da waɗansu sarakunan al’ummar Hausawa da sauran na kasassu mazauna cikin garin Legas da kewayenta.
Taron ya gudana ne a kan titin Oko Baba Abeokuta st Ibitimeta dake cikin garin Legas.
Bayan malamai sun kammala gudanar da addu’o’in nema wa Nijeriya da sauran ƙasashen da suka yi maƙwabtaka da ita ƙarin zaman lafiyar ne wakilin Jaridar Manhaja a Legas ya zanta da Sarkin Guragun na Jihar Legas domin jin ta bakinsa dangane da wannan taro, inda sarkin ya bayyana cewa haƙiƙa duba da cewa waɗansu lokutan ana samun ɗan rashin kwanciyar hankali a Nijeriya dama waɗansu sauran ƙasashen da suka yi makwabtaka da Nijeriya suka ga ya kamata a matsayin su na nakasassu kuma cikakkun ‘yan Nijeriya nagari suka ga ya kamata suma ɓangarensu na nakasassu su bai wa Nijeriya ta su gudummawar ta gudanar da addu’o’in neman a mincewar Ubangiji a wajen cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya da sauran ƙasashe maƙwabtanta baki ɗaya.
Sannan kuma ya buƙaci Gwamnatin Tarayyar da ta taimaka ta sama musu sana’o’in yi kamar tuƙin Keke Napep da sauransu.