An haɗa na’urar Wentian da na’urar Tianhe a sararin samaniya

Daga CMG HAUSA

Rahotanni daga ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin (CMSA) sun ce, bayan da aka yi nasarar harba na’urar Wentian, wani muhimmin ɓangare na farko na tashar binciken sararin samaniya, har ta shiga falaki cikin nasara, da misalin ƙarfe 3 da minti 13 na safiyar yau Litinin 25 ga wata ne, na’urar Wentian ta yi nasarar haɗewa da bangaren gaba na na’urar Tianhe a sararin samaniya, al’amarin da ya shafe tsawon awa 13.

Wannan shi ne karon farko da wasu manyan na’urorin binciken sararin samaniyar ƙasar Sin guda biyu, masu nauyin ton 20, wato Wentian da Tianhe, suka haɗe da juna a cikin falaki, kana karon farko da aka yi nasarar haɗa su, a yayin da ‘yan saman-jannati suke gudanar da ayyuka a cikin kumbo.

Har wa yau, sabbin rahotanni daga ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin (CMSA) sun ce , da misalin karfe 10 da minti 3 na safiyar yau Litinin 25 ga wata, ‘yan saman-jannatin ƙasar Sin wadanda suke aiki a cikin kumbon Shenzhou-14, sun yi nasarar shiga cikin na’urar Wentian.

Fassarawar Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *