An haɗa wutar gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta lokacin sanyi a Beijing

Daga CRI HAUSA

Larabar nan ne, aka haɗa wutar gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 daga harsunan wuta tara zuwa ɗaya a wurin ibadar aljannar duniya da ke birnin Beijing wato Temple of Heaven.

Ɗaya daga cikin harshen wutan, ya fito ne daga wurin gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta samo asali, wato Stoke Mandeville da ke ƙasar Birtaniya, daga bisani aka aika da shi zuwa birnin Beijing, don haɗa shi da sauran harsunan wutar guda 8 da suka fito daga yankunan gasar guda uku na Beijing, da Yanqing da kuma Zhangjiakou.

An dai fara miƙa wutar nan da nan, bayan da aka haɗa wutar bisa jigon “Wuta ta sama ta tara,” wadda ita ce mafi ƙololuwar samaniya. Jimillar masu miƙa wutar 565 ne za su shiga bikin, kashi 21 daga cikinsu kuma na da nakasa. Za kuma a kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanar da bikin miƙa wutar a cikin yankuna uku da za a gudanar da gasar, kafin a shiga da ita cikin filin gandun daji na wasan Olympic a ranar Alhamis da yamma, domin miƙa ta a cikin tsarin gudanar da gasar.

Za a fara gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 ne a ranar 4 ga watan Maris, za a kuma kammala a ranar 13 ga watan na Maris.

Fassarawa: Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *