An halaka ɗan binidgar da ya kashe DPO

*Jiragen sojoji ya sheƙa Dogo Umaru da ’yan ta’adda 41 barzahu

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta samu gagarumar nasarar sheƙa wasu gungun ƙasurguman ’yan bindiga zuwa barzahu, waɗanda suka kitsa kashe Babban Jami’in ’Yan Sanda na Yanki (DPO) a Jihar Katsina.

Hare-haren da jiragen NAF ya kai a jiya Alhamis ya samu nasarar halaka Dogo Umaru, wanda ƙusa ne a tafiyar babban ɗan bindigar nan, Bello Turji, wanda ake zargi da addabar yankin Arewa maso Yamma da ayyukan garkuwa da mutane da kuma kisan kiyashi. A tare da Umaru akwai ’yan bindiga 41 da ake kyautata zaton su ma sun sheqa lahira ba shiri.

Majiyoyin soja sun tabbatar da cewa, ajalin ’yan bindigar dajin ya sauka ne ƙauyen Magama da ke yankin Ƙaramar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina, inda aka yi ruwan wutar.

Bayanan sun nuna cewa, jami’an tsaron Nijeriya su na ta haƙon Dogo Umaru da yaransa ne tun bayan da ake zargin su ne suka kitsa harin da ya kai ga kisan DPO na Magama kuma suka raunata wani soja a kwanakin baya.

Dogo Umaru da mabiyan nasa sun yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare a kewayen yankin, inda suka yi sansanin kama-wuri-zauna a Makarantar Firamare ta Tsamben Dantambara, wacce suka kori kowa daga kusa da gurin, don mayar da makarantar matsuguninsu.

Wata majiya ta tabbatarwa da Blueprint Manhaja cewa, guda daga cikin jiragen sojan sama ya yi ta kai farmaki kan sansanin ’yan bindigar, waɗanda suka riƙa ƙoƙarin arcewa daga maɓoyar, a yayin da kuma wani jirgin yaƙin ya riƙa ragargazar waɗanda ke fitowa a gujen ya na yi musu ɗauki-ɗaiɗai.

Wata majiya a ƙauyen Tsamben Babare ta ce, wannan dabarar yaƙi ta kai ga halaka ’yan bindigar dajin aƙalla guda 42, ciki kuwa har da jagoransu, Dogo Umaru.

Wani jami’in leƙen asiri ya shaida wa majiyar Blueprint Manhaja cewa, da ma rundunonin sojan Nijeriya da sauran jami’an tsaro sun haɗa hannu wajen zafafa baza komarsu a ilahirin Yankin Arewa maso Yamma, don raunana ayyukan ta’addanci.

“A makon jiya ma, wasu hare-hare da jirgin Rundunar Sojan Sama da ke yankunan jihohin Kaduna da Neja sun halaka ’yan ta’adda da dama a kusa da Makarantar Koyon Aikin Soja (NDA) da ke Kaduna a wajenen Shadadi-Maundu,” inji shi.