Ma’aikatar Shari’a ta Koriya ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an hana Shugaban Ƙasa Yoon Suk Yeol fita daga ƙasa, bayan mako guda da kafa dokar ta ɓaci na ɗan gajeren lokaci.
A daren ranar 3 ga Disamba, Shugaba Yoon ya aika da rundunar sojoji na musamman da jiragen sama masu saukar ungulu zuwa majalisar dokoki, sai dai ‘yan majalisar sun yi watsi da dokar ta ɓacin da ya kafa, wanda hakan ya sa ya janye umarnin. Wannan matakin ya haifar da tashin hankali a ƙasar, inda jama’a suka yi zanga-zanga, suna kira da a sauke shi daga mulki.
A ranar Asabar, Shugaba Yoon ya tsallake ƙuri’ar tsige shi da aka gabatar a majalisa, duk da haka binciken da ake yi kan al’amuransa da na muƙarrabansa na cigaba da ƙarfafa.
Ana zargin Shugaban da hannu a yunƙurin tayar da tarzoma.
Ma’aikatar Shari’a ta tabbatar da cewa Shugaba Yoon ya zama shugaban ƙasa na farko a tarihin Koriya ta Kudu da aka hana fita daga ƙasa yana kan mulki. Wannan na cikin matakan bincike kan abubuwan da suka faru a makon da ya gabata.
Hakazalika, an hana tsohon ministan tsaro Kim Yong-hyun da tsohon ministan harkokin cikin gida Lee Sang-min fita daga ƙasa saboda rawar da suka taka a cikin al’amarin. Kim yana tsare a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da tuhuma kan Lee. Wannan ya ƙara sanya damuwa a fagen siyasar kasar.