Daga BELLO A. BABAJI
Ministan harkokin waje na ƙasar Isra’ila, Katz ya sanar da cewa an haramta wa Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres shiga Isra’ila.
Hakan na zuwa ne sakamakon rashin yin alla-wadai da harin da Iran ta kai wa Isara’ila a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 da kuma amabtan ta a matsayin wacce ke da alhaki da Sakataren bai yi ba duk da cewa ƙasashen duniya sun yi hakan.
Katz ya ce, duk wanda bai yi alla-wadai da harin da Iran ta kai wa ƙasarsu ba, bai halatta yi a shigo ƙasar ba.
Kawo yanzu ba a san ko ministan yana da ikon yin hakan ba kasancewar jami’an hukumomin shige-da-fice, da na ƙididdiga da kuma na kan iyaka sun ce ma’aikatar harkokin cikin gida ke da alhakin dakatar da wani daga shiga ƙasar, kamar yadda Hebrew Media Outlet ta ruwaito.