An hasko ɓacin ran mazan Somaliya a taron mata na Majalisar Ɗinkin Duniya

Ce-ce-ku-ce ya ɓarke a shafukan sada zumunta bayan da Ministan Iyali na Somalia Gen Bashir Mohamed Jama ya yaɗa hotuna kan ɗ na kansa da kuma wani namijin wakili da ke wakiltar Somaliya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan harkokin mata.

Fathiya Absie, wata fitacciyar marubuciya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil adama ta Somaliya ta shaida wa BBC cewa: “Abin kunya ne a ce gwamnatin Somaliya ta sanya maza a sahun gaba, masu wakiltar mata a taron.”

Wani babban ma’aikacin gwamnati ya shaida wa BBC cewa, wasu mata biyu su ma sun kasance cikin huɗu daga wakilan Somaliya a taron ‘Mata da Zaman Lafiya da Tsaro’ a New York, amma ba a saka su a cikin hoton ba.

Daga cikin wakilai 197 da suka yi rajista daga kasashe 57, 21 kawai ne maza.

An wallafa hotun da dama a dandalin twitter, wadda aka fi sani da ɗ, da suka nuna Gen Jama tare da mai ba shi shawara, tsohon ɗan majalisa Abdullahi Godah Barre; wani kuma ya nuna su a ɗakin taron tare da wani mutum, wanda aka shaida wa BBC cewa mataimaki ne.

Mohamed Bashir, wani babban ma’aikacin ma’aikatar iyali da ci gaban bil adama ta Somalia ya shaidawa BBC cewa, “Ba shi kaɗai ba ne namijin minista da ya halarta, akwai da yawa daga cikin ministoci maza, kamar Japan da Chana.”

“Wakilan mata biyu na Somaliya sun haɗa da Iman Elman, wata fitacciyar jami’ar soji, da Sadia Mohammed Nur, ma’aikaciyar gwamnati a ma’aikatar,” inji shi.

Rikicin ta yanar gizo ya sake haifar da suka ga matakin da gwamnati ta ɗauka a watan Yuli na sauya sunan ma’aikatar mata da kare haƙƙin bil’adama zuwa ma’aikatar iyali da ci gaban ‘yancin ɗan adam.

A wannan lokacin ne aka naɗa Janar Jama, wani babban hafsan soji da ya riƙe muƙamai da suka haɗa da shugaban hukumar leƙen asiri da na gidan yari, ya jagoranci ma’aikatar.

“Cire kalmar ‘mata’ daga taken ma’aikatar na nufin dunƙule gwagwarmaya da takamaiman buƙatun mata. Kalmar ‘iyali, ce ƙara bayyana hakan,” inji Ms Absie.