An ja layin yaƙin siyasa tsakanina da kai – Mataimakin Gwamnan Zamfara ga Gwamna Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rikicin siyasa a Jihar Zamfara ya ƙara ruruwa bayan da Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu ya ke gaya wa Gwamna Bello Matawalle cewa an ja layin yaƙi tsakanin su.

Da ya ke jawabi a ƙarshen zaɓen shugabannin jam’iyar PDP na jiha a ranar Litinin da ta gabata da daddare, mataimakin gwamnan ya ce “yanzu fa ba ɗaga ƙafa.”

“Da ga yau, an ja layin yaƙi. Idan an kashe mutane kuma gwamnati ta yi shiru, to mu za mu yi magana. Idan gwamnati ta ƙi buɗe makarantu, za mu yi magana.

“Hakazalika za mu magantu idan manoma su ka kasa zuwa gonakin su ko idan a ka ƙi ginawa al’umma tituna. Za mu ci gaba da sukar gwamnati a kan ba daidai ba daga yanzu har zuwa lokacin da za mu karɓi mulki,” inji Aliyu.

Haka zalika, Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwa a kan “irin gallazawa PDP” da a ke yi a jihar tun bayan da gwamnan ya sauya sheƙa zuwa APC.

Aliyu ya suffanta PDP a matsayin jam’iyya mai bin doka, inda ya nuna cewa kundin tsarin mulki ya bai wa jam’iyyar damar samuwa a Zamfara.

Ya yi alƙawarin gina sabuwar PDP mai cike da zaƙaƙuran matasa ma su ilimi.

Ya ƙara da cewa hakan shi zai sanya jam’iyyar ta ƙwaci mulki a Zamfara a 2023.

Aliyu ya kuma yi kira ga Gwamna Matawalle da ya sakar wa PDP mara ya maida hankali a kan magance matsalolin da ke damun jihar.