An jigbe gawargawaki tsawon shekara huɗu a Cibiyar Lafiya da ke Keffi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Hukumar gudanarwar babbar Cibiyar Lafiya ya Tarayya, wato Federal Medical Centre, da ke garin Keffi, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa, ta ce, a yanzu haka akwai kimanin gawarwakin mutane 10 da suke ɗakin adana gawarwaki a cibiyar, waɗanda suka shafe shekaru huɗu a ajiye. 

Babban jami’in hulɗa da jama’a na cibiyar Mohammed Adamu ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da Wakilin Blueprint Manhaja dangane da lamarin a ofishinsa da ke cibiyar ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairun da ake ciki. 

Ya ce, waɗannan gawarwarki waɗanda ba a san ko su wanene ba, ba a kuma san ‘yan uwansu ba, jami’an ‘yan sanda masu sintiri da takwarorinsu na hukumar kare haɗura ne suka kwaso su zuwa cibiyar a ranaku da lokuta daban-daban kimanin shekaru 4 da suka gabata wato tsakanin shekarar 2018 da 2019 da kuma 2020. Kuma har yanzu suna kwance a ɗakin adana gawarwaki na cibiyar. 

A cewarsa wannan lokaci ya riga ya wuce adadin lokaci wato na wata 6 da doka ta tanadar ta kuma amince a bar ire-iren gawarwakin a ɗakin adana gawarwakin. 

Dangane da mataki na gaba da cibiyar za ta iya ɗauka a kan lamarin sai Mohammed Adamu ya ce “to a nan ina so in jawo hankulan al’umma baki ɗaya a ciki da wajen jihar nan baki ɗaya in kuma sanar da su cewa a yanzu mun bada dama da izini wa kowa ya zo ya shiga ɗakin adana gawarwakin musamman waɗanda wani nasu ya rasu ko ya ɓace ba su gan shi ba tsakanin waɗannan lokuta da na ambato. 

Ya ƙara da cewa “za su iya ziyartar asibitin nan don gudanar da bincike a kan hakan. Sannan kuma bayan wannan sanarwa ina mai tabbatar maka cewa nan gaba kaɗan zai zame wa cibiyar nan wajibi ya yi wa duka mamatan jana’iza a lokaci guda wato abinda ake kira mass burial kenan a turance,” inji shi. 

Ita dai wannan cibiyar, cibiya ce da Gwamnatin Tarayya ta kafa a garin Keffi kamar yadda suke a wasu jihohin ƙasar nan don samar da magunguna cikin gaggawa ga majinyata musamman waɗanda haɗuran ababen hawa a manyan tituna ya rutsa da su da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *