An kafa ƙungiyar bada ilimin sana’o’i ta Sin da Afrika

Daga CMG HAUSA

A ranar 11 ga wata, ƙungiyar mu’ammala ta fuskar ba da ilimi ta ƙasar Sin, ta kira wani taro na ingiza shirin ba da ilimin sana’o’i tsakanin Sin da Afrika, kuma taron kafa ƙungiya a wannan fanni ta kafar bidiyo da a zahiri, don tabbatar da shawarwarin haɗin kan Sin da Afrika, da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika.

Mataimakin daraktan sashin hadin kan ƙasa da ƙasa, da yin mu’amala na hukumar ba da ilmi na Sin Jia Peng, ya taya murnar kafuwar ƙungiyar. Ya kuma ce makomar nahiyar Afrika ita ce matasa, kuma mafitar matasa ita ce samun ilimi.

Ya ce gwamnatin Sin ta daɗe tana ɗora matuƙar muhimmanci kan haɗin kan ɓangarorin biyu a wannan fuska, musamman ma a fannin ba da ilimi na sana’a, abin dake da makoma mai haske wajen haɗin kansu.

Sin na fatan kafa tsari mai yakini da ƙasashen Afrika cikin dogon lokaci, don goyon bayan shiri mai taken “Makomar Afrika: haɗin kan Sin da Afrika kan ba da ilmi na sana’a”, ta yadda za a horas da ƙwararru a fannin samar da kayayyaki da raya tattalin arziki na yanar gizo, da dai sauran sabbin sana’o’i.

Mai Fassara: Amina Xu