Daga AMINA YUSUF ALI
Mata masu gudanar da kasuwanci a shafukan intanet a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun kafa wata ƙungiya mai suna Women Online Vendors Association (WOVA) da za ta samar da aminci tare da kyautata hulɗa tsakanin mai saye da mai sayarwa.
Shugabar ƙungiyar ta WOVA Hajiya Ayat Uba Adamu ta bayyana wa majiyarmu cewa sun kafa ƙungiyar ne da nufin haɗa kan matan da suke gudanar da kasuwancinsu a shafukan intanet tare kuma da samar da aminci tsakanin masu saye da sayarwa.
“Samar da aminci tsakanin masu saye da sayarwa ta hanyar karkaɗe ɓata gari da su ke neman kashe kasuwancin yanar gizo, sanan samun masalaha tsakanin mu da direbobi da wayarwa da kuma ilmantar da Mata harkar kasuwancin zamani wato Digital Marketing, da ƙarfafa wa junanmu gwiwa kan kasuwancinmu, wanda idan ba a dunƙule mu ke ba dukkan wanan abin ba zai samu ba“
Haka kuma Ayat Uba Adamu ta ce babban burin ƙungiyar ta WOVA shi ne haɗa kan mata masu kasuwanci da ke sassan Najeriya da ma makwaftan ƙasashe domin warware irin matsalolin da kasuwancin na zamani ke fuskanta.
“Babban burin wannan ƙungiya shi ne jawo dukkan Mata masu kasuwanci a yanar gizo a ko ina suke a Nigeria, kai har makwaftan ƙasar nan da su zo mu haɗu inuwa ɗaya domin warware matsalolin da kasuwancin yanar gizo ke fuskanta.
Ta kara da cewa “Kuma muna da burin mu dinga ƙara wa junan mu ilmin kasuwancin zamani wato Digital Marketing domin haɓɓaka tattalin arzikin mu da ma ƙasa gaba ɗaya”
Hanyoyin sadarwar zamani na Intanet dai sun yi tasiri sosai wajen gudanar da kasuwanci a tsakanin mata da matasa a sassan Najeriya. Kuma wannan tsari na kasuwancin zamani ya kawo sauki ta hanyoyi da dama tsakanin mai saye da mai sayarwa.