Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a faɗin jihar.
Cikin sanarwar da ta fitar ranar Laraba ta bakin Kwamishinanta, rundunar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro da kiyaye doka a faɗin jihar.
Sanarwar ta ce al’ummar Kano su sani cewar, an riga da an tura jami’an da suka dace a sassan jihar domin tabbatar da an yi wa dokar hana zirga-zirgar biyayya.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya ce dokar ta fara aiki ne daga ƙarfe 6 na yamma na ranar Laraba, 20 ga Satumba, zuwa 6 na yamma na Alhamis, 21 ga Satumba.
Ya ce ƙara da cewa, duk wanda aka kama da laifin yi wa dokar karan tsaye, zai fuskanci fushin hukuma.
Kafa dokar ba ya rasa nasaba da hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan jihar ta yanke a ranar Laraba, inda ta ce Yusuf Gawuna ne zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar amma Abba Kabir ba.