An kai hari wata sakandire a jihar Katsina a yayin da shugaba Buhari ke hutu a jihar

Masu garkuwa da mutane sun kai hari wata sakandire a garin Kankara na jihar Katsina.

Wadanda suka ganewa idon su abinda ya faru, sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutane, sun kutsa cikin makarantar ne da dare, in da suka harbi mai gadin makarantar, kuma suka yi kan mai uwa da wabi da bindigogi a dakunan kwanan daliban.

A halin da ake ciki dai ba a gama tantance yawan daliban da suka kwasa ba, ba kuma wasu alkaluma da suka nuna yawan daliban da suka jikkata ko suka rasu a yayin wannan hari.

Har dai yanzu hukumomi a jihar Katsina ba su ce komai akan wannan hari ba. Haka ma jami’an yan sanda sun yi gum da bakin su.

A halin da ake ciki dai yanzu, yan sanda sun kwashe sauran daliban da ke makarantar, zuwa babbar sakatariyar karamar hukumar domin kula da su.

Wannan harin dai ya zo a daidai lokacin da shugaba Buhari ke wani hutun mako a garin Daura da yake jihar ta Katsina.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*