An kai malama kotu bisa zargin cin zarafin ɗaliba ‘yar shekara tara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata malama, Aderonke Makonde, a ranar Laraba aka gurfanar da ita a wata kotun majistare da ke Ikeja a Jihar Legas bisa zargin laifin cin zarafin wata ɗalibar makarantar mai shekara tara.

Rundunar ‘yan sanda ce ta gurfanar da Makonde, mai shekaru 35 kuma malama a makarantar Westgate Land Emperial Creche Nursery and Primary School da ke Mushin, Legas bisa laifin cin zarafi.

Sai dai matar ta musanta zargin da ake mata.

Lauyar masu shigar da ƙara, DSP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Makonde ta ci zarafin ɗalibar ne ta hanyar “shasshauɗa mata bulala a jikinta ba tare da tausayi ba tare da yi mata rauni a jiki.”

Ta ce surutu a aji shi ne kaɗai laifin ɗalibar.

Ajayi ta ce laifin malamar ya saɓa wa sashe na 172 na dokar laifuka ta Legas, 2015.

Alƙalin kotun, E. Kubeinje, ta bada belin wacce ake tuhumar a kan kuɗi Naira dubu 50 tare da tsayayyu biyu kowannensu tare da shaidar biyan haraji da kuma sahihin adireshi.

Daga baya Kubeinje ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 7 ga watan Yuni.