An kai wa Shugaban Ƙasar Mali hari a masallacin idi

Daga WAKILINMU

Bayanan da Manhaja ta samu da rana nan daga ƙasar Mali, sun nuna an kai wa Shugaban Ƙasar, Assimi Goïta, hari a masallacin idi yayin sallar Idul Kabir a yau.

Wasu mutum biyu ne ɗauke da wuƙa suka kai wa shugaban hari a masallacin idi na Bamako, babban birnin ƙasar.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan ko shugaban ya ji rauni sakamakon harin, amma an yi nasarar ɗauke shi daga wurin.

Idan ba a manta ba Colonel Goita shi ne wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya faru a ƙasar a Agustan bara inda aka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita

Ministan Harkokin Addini na Ƙasar, Mamadou Kone, ya shaida wa jaridar AFP cewa, “Wani mutum ne ya yi yunƙurin halaka shugaban ƙasar da wuƙa, amma an daƙile harin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *