Daga BASHIR ISAH
Bayanai daga Jihar Adamawa sun ce an damƙe wani da ake zargin ɗan Boko Haram bayan da ya yi yunƙuri kai harin bom a gidan toshon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da ke Yola, babban birnin jihar.
An ce an kama wanda ake zargin, Jubrila Mohammed ne a ranar Lahadi bayan da aka lura da take-takensa.
Mohammed ya faɗa wa ‘yan sanda cewa, da shi aka shirya yadda za a kai harin bom a gidan Atiku da wani ɓangare na American University of Nigeria da kuma Babban Masallacin Modibbo Adama duk a Yola.
Majiyarmu ta ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yan Sandan Adamawa don zurfafa bincike.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Reno Omokri wanda ya kasance masoyin ɗan takarar shugabancin ƙasa na PDP a babban zaɓen 2023 da ya gabata.
Omokri ya yi kira ga hukumomin tsaro da a yi cikakken bincike kan batun, sannan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta tsananta bai wa Atiku tsaro.