An kama fasto yana kai wa ƴan ta’adda bindiga a Filato da Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda ta yi nasarar kama wani fasto da wasu da ake zarginsu da hannu a kai wa ƴan ta’adda bindigu a Jihohin Kaduna da Filato da wasu yankunan Jihar Nasarawa.

Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya bayyana hakan a lokacin da aka gurfanar da waɗanda ake zargin a makon da ya gabata a Abuja.

Ya ce jami’an sirri na IRT a Filato sun kama mutanen ne a wurare mabanbanta waɗanda mambobi ne na tawagar safarar haramtattun bindigu.

A yayin atisayensu ne suka gano wani rumbun makamai da ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su.

Waɗanda jami’an IRT’n suka kama sun haɗa da Joseph Tata mai shekaru 33 da Alias Muazu daga ƙauyen Zumu a ƙaramar hukumar Mikang ta Jihar Filato wanda kama shi ya taimaka wajen kamo Victor Ali-Pam, ɗan shekara 33, Abua Yusuf, Bako Isa, da Salamatu Ilya ƴar shekara 34, wadda ke zaune a Jos.

Haka kuma a ranar 28 Junairu, sun kama Musa Ari daga Tambegua a Jihar Kaduna da Britus Tom daga Vom a Filato.

Kazalika, ya ce an ƙwato muggan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK47 guda takwas da ƙananu ƙirar ‘Pistol’ da mazubin harsasai da dai sauransu.

Har’ilayau, Adejobi ya bayyana cewa an kama su ne akan hanyarsu ta kai makaman ga ƴan ta’adda dake ayyukansu a Filato da Kaduna da kewaye.