An kama fitaccen kwamandan ’yan fashin daji a Zamfara da bindigogi 200

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce an kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Katare a ranar Asabar da ta gabata.

Shinkafi ya bayyana hakan ne ga manema labarai, inda ya ƙara da cewa Katare yakan gudanar da hare-haren sa ne a kusa da Lambar Bakura-Tureta da dajin Raba a jihar Sakkwato.

A cewarsa, abubuwan da aka samu daga hannunsa akwai bindigogin AK-47 guda 200 a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa zuwa wani dajin da ke jihar.

Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya ce kwamandan ‘yan fashin bai wuce shekara 30 ba, kuma tuni ya amsa laifinsa na samar da makamai daga Jamhuriyar Nijar tare da yin amfani da su wajen gudanar da munanan ayyuka.

Ya bayyana cewa, shugaban ‘yan bindigar yana addabar jama’a a kan hanyar Sakkwato zuwa Talata Mafara da kuma wani yanki na ƙananan hukumomin Rabah da Maradun na jihohin Sakkwato da Zamfara.

Shinkafi ya koka da yadda wasu ke ƙoƙarin sanya siyasa a cikin rashin tsaro da jihar ke fuskanta, don haka akwai buƙatar a ƙara ƙaimi wajen ƙoƙarin Gwamna Bello Mohammed Matawalle na ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.

“Ƙalubalen tsaron da jihar Zamfara ke fuskanta, ya shafi dukkanin Malamai, ‘yan siyasa da suka haɗa da PDP, APC, APGA ba tare da la’akari da irin aƙidun siyasar da muke da ita a jihar Zamfara ba,” inji Shinkafi.

Ya kuma buƙaci mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk wani motsi da wasu mutane ke yi a yankunansu ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa.