Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jami’an ’Yan Sandan Dubai sun kama wani mabaraci da ya bayyana a matsayin wanda aka yanke wa ƙafa, ɓoye da tsabar kuɗi $81k kwatankwacin Naira miliyan 37.3 a cikin jabun ƙafafun roban.
A cewar jaridar Gulf News, mutumin da ya shiga ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da takardar bizar ziyara an kama shi ne a ranar Alhamis 16 ga Maris, 2023, inda yake roƙon sadaka a kusa da masallatai da kuma wuraren zama.
An tattaro cewa mabaracin bayan kama shi an miƙa shi zuwa gaban kotu na Dubai.
’Yan sandan Dubai sun gargaɗi jama’a da kada su ruɗu da mabarata da ke ƙirƙirar dabaru daban-daban don neman tausaya daga gare su.