An kama matsafa shida kan yunƙurin kashe basarake a Ogun

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an ‘yan sanda a Jihar Ogun da ke Nijeriya sun damqe wasu mutum shida yayin da suke ƙoƙarin kashe wani basarake.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar na cewa mutanen da aka kama sun haɗa da Michael Ayodele da Monday Samuel da Ademola Matthew da Hammed Jelili da Ogundele Ojeh da kuma Sunkanmi Fadina.

Kakain rundunar ‘yan sandan Abimbola Oyeyemi, ya ce rundunar ta sami rahoto daga sarki G.O. Olukunle na garin Oja Odan da ke ƙaramar hukumar Yewa ta Kudu ta Jihar Ogun da misalin ƙarfe 4:25 na yamma cewa wasu matsafa na shirin kashe shi a cikin fadarsa.

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa jami’ansu sun isa wurin kuma bayan musayar wutar sun kama shida a cikin matsafan:

“Bayan mun bincike su, matsafan sun tabbatar mana cewa ɗan basaraken ne ya yi hayarsu domin su kashe mahaifin nasa saboda wata matsala da ke tsakanin sarkin da mahaifiyarsa.”