An kama mutane 34 yayin da aka fara farautar mabarata da ƴan bola a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI

Aƙalla mutane 34 ne aka kama bayan da hukuma a birnin tarayya Abuja ta ƙaddamar da rufdugu akan mabarata da ƴan bola da makamantansu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba su wa’adin tattara komatsansu su fice daga birnin wanda ya ƙare a ranar Lahadi.

Cikin waɗanda aka kama akwai mabarata 15 da kuma ƴan bola 19 waɗanda za a miƙa su gidan gyaran tarbiyya da ke Bwari don su karɓi horo.

Jami’an da suka gudanar da atisayen sun haɗa da; sojoji, ƴan sanda, DSS, Civil Defence da wasu hukumomin tsaro inda aka baza su don farautar ire-irensu a ƙarƙashin gadoji da makamantansu.

Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Olatunji Disu ya bayyana atisayen a matsayin aiki ne na ƙasa baki ɗaya, ya na mai kira ga jami’an da ke gudanar da aikin su kasance masu nuna ƙwarewa.

Ya ce za ɗauki sati biyu ana gudanar da atisayen a karon farko inda daga bisani za yi nazari game da sakamakon da hakan ya bayar tare de ɗaukar mataki na gaba.

Haka ma za a tashi ƙananan ƴan kasuwa da ke sana’o’insu a gefen titina da wasu wuraren da ba su dace ba yayin atisayen.

A nasa jawabin, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce gwamnatinsa za ta samar da tsarin tsaro da zai fitar da mabarata a Abuja baki ɗaya.

Wike ya ce ya zama wajibi a kore su kasancewar sun karaɗe manyan titunan birnin, ya na mai bayyana Abuja a matsayin birnin da Nijeriya ke da ita da za ta nuna wa duniya.