An kame ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya fiye da 10 a Habasha

Jami’an tsaron Habasha sun kame ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya fiye da 12 dake aiki a ƙasar, kamar yadda jami’an agaji suka tabbatar.

Bayanai sun ce an kame jami’an ne a birnin Addis Ababa, yayin wani samame da aka kaiwa ‘yan ƙabilar Tigray a ƙarƙashin dokar ta-ɓaci.

Ɗaya daga cikin majiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya da suka tsegunta labarin kamen, ta ce an ɗauke wasu daga cikin jami’an da aka kame ne a gidajensu.

Tuni dai wata mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva ta sanar da mika buƙatar sakin jami’an nasu ga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Habasha.

A makon da ya ƙare, gwamnatin Fira Minista Abiy Ahmed ta sanar da kafa dokar ta-ɓaci ta tsawon watanni shida a faɗin Habasha, sakamakon fargabar da ake yi na cewa mayaƙan ƙungiyar ‘yan tawayen ‘Tigray People’s Liberation Front’ da ƙungiyar ‘yan tawayen ‘Oromo Liberation Army’ (OLA) za su iya kutsawa babban birnin ƙasar.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ciki har da ‘Amnesty International’ dai sun yi Allah wadai da dokar ta-ɓacin, wadda ke ba da damar bincikar duk wanda ake zargi da tallafawa ƙungiyoyin ta’addanci tare da tsare shi ba tare da izini ba.

Ana dai takun saƙa tsakanin gwamnatin Fira Minista Abiy da Majalisar Ɗinkin Duniya a tsawon lokacin da aka shafe ana gwabza yaƙi sojojin gwamnati da ‘yan tawayen TPLF, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da jefa wasu dubban cikin mummunan yanayi na yunwa.

A ƙarshen watan Satumba ma’aikatar harkokin wajen Habasha ta sanar da korar wasu manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya bakwai saboda katsalandan cikin harkokin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *