An kammala aikin gini mafi tsayi a gabashin Afirka

Daga CRI HAUSA

A jiya Lahadi, an kammala aikin ginin sabuwar helkwatar bankin kasuwancin ƙasar Habasha, aikin da kamfanin ƙasar Sin ya ɗauki nauyin ginawa, wanda kuma ya kasance gini mafi tsawo a gabashin nahiyar Afirka. Firaministan ƙasar Habasha Abiy Ahmed Ali da jakadan ƙasar Sin a ƙasar Mr. Zhao Zhiyuan sun halarci bikin ƙaddamar da ginin.

Ginin dai ya kasance a cibiyar kasuwanci ta birnin Addis Ababa, kuma kamfanin CSCEC ne ya fara ɗaukar nauyin ginawa tun daga watan Yulin shekarar 2015.

A jawabin da ya gabatar, firaministan ƙasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya taya murnar ƙaddamar da ginin, inda ya ce, yadda aka ƙaddamar da wannan kyakkyawan ginin a daidai lokacin cika shekaru 80 da kafuwar bankin kasuwancin ƙasar ya shaida aniyar ƙasar ta zamanintar da harkokin bankinta.

Sai kuma babban daraktan bankin kasuwancin Habasha ya ce, sabon ginin zai inganta aikin bankin, tare da samar da fasahohin zamani ga ɓangaren gine-gine na ƙasar.