An kammala musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa a Bauchi

Daga MU’AZU HARƊAWA a Bauchi

An kammala gasar musabaƙar karatun Alƙu’ani ta ƙasa kashi na 36 da aka gudanar cikin kwanaki tara a jihar Bauchi, inda jihar Borno ta zo na farko, yayin da Zamfara na biyu.

Gasar wacce aka fara gudanar da ita cikin shekarar 1986 a ƙarƙashin Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato; Jihar Kano ce kan gaba wajen samun nasara mafi rinjaye a tsawon shekarun.

Amma a bana Alaramma Abba Sanyinna Goni Muktar daga jihar Borno shi ne ya zo na farko, sai kuma Malama Haulatu Aminu Ishaq daga jihar Zamfara ta zo ta farko a mata.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya bada Naira miliyan shida ga gwarazan shekarar kowa miliyan uku, inda aka sake ba kowa Naira miliyan biyu a matsayin kyautar kwamitin gasar.

Haka shi ma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya bayar da Naira miliyan goma ga dukkan ɗaliban da suka shiga gasar da kuma Naira miliyan goma ga wanda suka samu nasara, sai kuma Naira miliyan biyar ga alƙalan gasar.

Haka kuma Gwamna Bala Mohammed da Sarkin Musulmi sun ɗauki nauyin karatun wata ƙaramar yarinya da ta shiga gasar har zuwa karatun jami’a.

Farfesa Salisu Shehu mataimakin shugaban Jami”ar A-istiqama da ke Sumaila shine baƙo mai jawabi a wajen rufe gasar, ya ja hankalin iyaye da su himmatu wajen bayar da ilmin addini da nazarin littafi mai tsarki don samun ingancin addini da tarbiyya a zukatan matasa.

Shi ma Mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa L.S. Bilbis ya bayar da kyautar Naira miliyan guda ga ɗaliban gasar kuma ya ja hankalin wanda suka shiga gasar da wanda ya yi nasara da wanda bai yi ba ko ya ɗauki kansa a matsayin wanda ya samu nasara.

Ɗalibai 328 suka shiga gasar karatun da ake gudanarwa a kowace shekara, daga bisani wanda suka samu nasara kuma sune za su shiga gasar ta duniya a wata ƙasar musulmi.

Gwamna Bala da mai ɗakinsa Hajiya Lami Bala Mohammed sune suka naɗa gwarazan shekarar ta bana suka kuma hannanta musu cekin kuɗaɗen da suka samu a yayin nasarar musabaƙar ta bana.