An kammala taron tattauna zaman lafiya na Sin da kusuwar Afrika karo na farko

Daga CMG HAUSA

An kammala taron zaman lafiya da samar da ingantaccen shugabanci da ci gaba na Sin da kusurwar Afrika karo na farko a ranar Talata a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha, inda aka yi kiran haɗin gwiwa don cimma muradun bai ɗaya na shiyyoyin.

Mahalarta taron na kwanaki biyu da aka kammala, sun tattauna tare da fidda sanarwar haɗin gwiwa kan wasu muhimman batutuwa goma sha biyu.

Sanarwar haɗin gwiwar ta bayyana cewa, shiyyar kusurwar Afrika wato HOA, wani muhallin zama ne ga al’ummar dake shiyyar, kana ana buƙatar samun tabbatar da zaman lafiyar shiyyar, da kwanciyar hankali, da ci gaba, sannan neman makoma mai kyau shi ne muhimmin ginshiki na moriyar dukkan ƙasashen duniya kuma shi ne babban muradi na dukkan al’ummar shiyyar.

Bugu da ƙari, sun bayyana aniyarsu na samun kyakkyawan shugabancin siyasa, da ɗaukar ƙwararan matakan gina cigaba, da kawar da rashin fahimta da rashin jituwa a tsakanin ƙasashen shiyyar, da ƙoƙarin neman zaman lafiya ta hanyar tattaunawar sulhu don cimma nasarar sauƙaƙa yanayin tsaro a ƙasashen shiyyar.

Ƙasashen shiyyar sun kara yabawa ƙasar Sin sakamakon ɓullo da wannan taro, da nufin kyautata makomar zaman lafiyar kusurwar Afrika, da samar da shugabanci na gari da ci gaba, da yadda ƙasar ke ƙoƙarin tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da muradun ci gaban ƙasa da ƙasa, da shawarwarin tabbatar da tsaron ƙasa da ƙasa.

A cewar sanarwar haɗin gwiwa, ƙasar Sin ta tabbatar da aniyarta na yin amfani da shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya da aiwatar da sakamakon da aka samu a taron kolin FOCAC da manufofin cigaban ƙasashen shiyyar.

Mai fassarawa: Ahmad