An Karrama Zabiya Salmai Albasu

A jiya ne, gwamnatin jihar Jigawa ta karrama tsohuwar mawakiya, kuma jamiar wayar da kai a fannin ilmi, zabiya Salmai Albasu a garin Gumel.

A yayin wannan karramawa, kwamishinan Ilmi na jihar, ya bayyana ce wa an sauya sunan sakandiren je ka ka dawo ta Albasu daga yau, zuwa Salmai Babandi.

Zabiya Salmai Albasu dai ta bayar da gudunmawa a zamanin gwamnatin Alhaji Audu bako, wajen wayar da kan mutane su tura yara makarantun boko. Wakokin ta kuma sun shahara a fagen noma, ilmi da zamantakewa.

Taron dai ya samu halartar daruruwan jama’a daga sassan jihar.

In ba a manta ba, a watannin baya ma, wani dan jarida maisuna, Jafar Jafar yayi wani gangami na gidauniya, domin a tallafawa wata tsohuwar mawakiyar mai suna Zabiya Magajiya Dambatta. Wanda kuma a halin yanzu, tuni an kammala gina mata gida da kuma samar ma ta da ababen more rayuwa.

Zabiya Salmai Albasu

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*