An kashe ƴan jarida sama da 100 a yaƙin Gaza

Wani bincike na haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai suka gudanar ya yi ƙarin haske a kan yadda sama da Falasɗinawa ƴan jarida da ma’aikatan yaɗa labarai 100 suka mutu a yaƙin Gaza, duk da cewa suna sanye da taguwar da ke nuna cewa aikin jarida suke yi.

An shafe watanni huɗu kafin a ƙarƙare wannan bincike da tawagar ƴan jarida ta gudanar a ƙarƙashin kamfanin binciken na Forbidden Stories, wanda ta kunshi ƴan jarida 50 daga kafafen yaɗa labarai 13, ciki har da kamfanin dillancin labaran Faransa, The Guardian da kuma Arab Reporters for Investigative Journalism.

Tawagar ta yi nazari ne a kan hare-haren da ya shafi ƴan jarida da kafafen yaɗa labarai tun bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙi a kan Zirin Gaza, a matsayin martani a kan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

 A saƙonsa na shafin gabatarwa, shugaban kafar binciken ƙwaƙwaf ta Forbidden Stories, Laurent Richard ya ce mutuwar ƴan jarida sama da 100 a yayin wannan yaƙi duk da cewa suna sanye da rigar aiki na nuna cewa wannan riga ba ta ba su kariya, a maimakon haka ma sai dai ta jefa su cikin haɗari.

Carlos Martinez de la Serna, na ƙungiyar kare ƴan jarida ta duniya CPJ, ya bayyana kaɗuwarsa a game da adadin ƴan jarida da suka mutu a wannan yaƙi.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ba da gangan ne waɗannan hare-hare suka rutsa da ƴan jarida ba, yana iya yiwuwa su na sansanonin soji ne a lokacin aukuwarsu.