Sojoji sun harbe wani da ake zargi da yunƙurin sace akwatin zaɓe har lahira a rumfar zaɓen Bajida 001 cikin Ƙaramar Hukumar Fakai a Jihar Kebbi.
Bayanai daga yankin sun ce, an harbe matashin ne a lokacin da yake ƙoƙarin ƙwace akwatin zaɓe daga hannun jami’an zaɓe yayin zaɓen cike giɓi da INEC ta shirya a ranar Asabar.
An ce ɓata-garin ya yi basajar shi jami’in tsaro ne domin samun damar aikata mummunan nufinsa.
Haka nan, an yi zargin ya yi yunƙurin ƙwace bindigar wani soja a rumfar zaɓen kafin daga bisani aka alburshe shi har lahira.
A cewar ganau, “Shi da abokansa suka zo rumfar zaɓen inda suka yi ƙoƙari ƙwace akwatin zaɓe a lokacin da jami’an INEC ke ƙoƙarin tafiya cibiyar tattara sakamakon zaɓe.
“Ƙoƙarin da jama’a suka yi don dakatar da shi ya ci tura, kuma ya yi ƙoƙarin ƙwace bindigar wani soja daga nan wani sojan ya ɗauke shi da bindiga.”