An kashe wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda rikicinsu da ’yan acaɓa a safiyar Asabar a yankin Agege da ke Jihar Legas.
’Yan sanda sun ɗora laifin kisan a kan wasu ’yan acaɓa da ake zargin muna da hannu a lamarin.
Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba ya jagoranci tawagar ’yan sanda ne zuwa wajen da wani hatsari ya auku a mahaɗar WEMCO a yankin Agege.
Rahotanni sun ce ’yan sandan sun je ne domin su cire wata motar dakon kaya da ta buge wani ɗan acaɓa, amma sauran ’yan acaɓar suka yi musu tirjiya, inda suka yi ƙoƙarin ƙone motar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce farmakin da aka kai wa ’yan sandan ba lamari ba ne na wasa ba.
Ya bayyana cewa ’yan sanda sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:40 na asuba a ranar Asabar, dangane da wani hatsarin wani ɗan acaba da wata motar dakon kaya.
Binciken farko ya nuna cewa ɗan acaɓar ne ya cikin gudun wuce ƙima ya doki motar, kuma aka yi rashin sa’a ya rasa ransa.
Lokacin da ’yan sandan suka isa wajen, sun tarar da tarin masu babura.
A yayin da jami’an suke ƙoƙarin cire motar daga wajen, masu baburan suka kai musu hari.
ɗan sandan mai shekara 46, ya samu rauni a kansa, kuma ya mutu nan take, yayin da direban motar ya tsere.
An kama mutane biyar kawo yanzu, kuma ’yan sanda suna cigaba da farautar sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.