An kashe kwamandojin ISWAP

Daga BASHIR ISAH

Sojojin Nijeriya sun kashe wani babban kwamandan mayaƙan ISWAP tare da wasu mayaƙansa a wani harin ramuwar gayya da suka kai wa mayaƙan a yankin Askira-Uba na jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna mayaƙan na ISWAP sun kai wa so’joji hari don rama ragargazar da suka yi musu da jirgin yaƙi a Juma’ar da ta gabata tare da kashe musu mambobi da dama, wanda hakan ya yi ajalin Brigadier-General Dzarma Zirkushi a yankin Chibok tare da wasu sojoji su uku a ƙauyen Bungulwa kusa da Askira Uba a ranar Asabar.

An ce dakarun sun samu nasarar kashe jigon ISWAP ɗin ne bayan da suka jaya baya sannan suka sake sabon shiri kafin daga bisani suka afka wa ‘yan bindigar a yankin Askira Uba.

Wata majiya daga rundunar sojojin ta tabbatar da kashe ‘yan bindigar sama da mutum 30 a ranar Asabar, kuma baki ɗaya an gano gawarwakinsu. Tare da cewa har yanzu akwai sojoji na ci gaba da aiki a dajin Askira.

Majiyar ta ƙara da cewa, sojojin sun lalata motocin yaƙi mallakar ISWAP da dama yayin artabun.

A hannu guda, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yaba tare da jinjina wa sojojin Nijeriya bisa wannan nasarar da suka samu da kuma irin sadaukar da rai da sukan yi don kare ƙasa da al’ummarta.

Zulum ya yi wannan yabo ne cikin wata sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, inda ya sara wa dakarun da sauran dakarun maƙwabta da suka haɗa karfi da ƙafe wajen fatattakar mayaƙan ISWAP.