An kashe limami ɗan luwaɗi bayan jagorantar auren ƴan maɗigo

Daga BELLO A. BABAJI

An harbe wani babban malami da ya shahara a harkar luwaɗi mai suna Muhsin Hendricks a ƙasar Afirka ta Kudu, bayan jagorantar wani auren jinsi na ƴan maɗigo.

Hendricks mai shekaru 57, mutum ne da ya samar tare da jagorantar wani masallaci a Cape Town musamman don musulman da aka mayar da su saniyar ware waɗanda daga ciki akwai ƴan auren jinsi, wato ‘LGBTQ+ Community’.

A safiyar ranar Asabar ne aka kashe limamin a lokacin da ya ke tafiya zuwa wani gari a wata mota a birnin Gqeberha dake Kudancin ƙasar.

Ana zargin cewa an harbe shi ne a lokacin da ya ke hanyar dawowa daga ɗaura auren ƴan maɗigon.

Mutuwar limamin ta sanya ƴan LGBTQ cikin jimami ganin yadda mambobi a sassa daban-daban na duniya suka yi ta nuna alhini da jajentawa.

A shekarar 1996 ne Hendricks ya bayyana wa duniya ƙarar cewa shi ɗan luwaɗi ne, lamarin da ya tada ƙura acikin al’ummar musulmi a Cape Town da wasu sassa.

Daga bisani, ya kuma samar da masallaci mai suna Masjidul Ghurbaah inda ya ta yaɗa manufofinsa don ya samu karɓuwa a hannun jama’a.