An kashe malamin Jami’ar Maiduguri ta hanyar daɓa masa wuƙa

Daga BASHIR ISAH

Lamarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta gabata inda aka bi Dokta Kamar Abdulkadir har cikin ofishinsa aka daɓa masa wuƙa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Marigayin na malanta ne a Sashen Physical Health Education na jami’ar, kuma shi ne Jami’in Kula da Jarrabawa na tsangayarsu.

Mai magana da yawun jami’ar, Farfesa Danjuma Gambo, ya tabbatar wa da Jaridar News Point Nigeria da faruwar lamarin. Inda ya ce, da yammacin ranar Lahadi ne aka kashe malamin.

Ya ƙara da cewa, duk dai ba a kai ga tsare kowa ba kan batun, amma ‘yan sanda da takwarorinsa sun fara bincike kan kisan.

Bayanai sun nuna cewa marigayin ya tafi ofishinsa a wannan rana ne domin ƙarasa wasu ayyukan da ke kansa.

Wani abokin aikin marigayin ya ce, “Mummunan kisa suka yi masa, sun yi amfani da wuƙa da hamma ne wajen kashe shi. Haka nan sun tafi da motarsa.

“Kodayake wasu na alaƙanta kisan da muƙamin da yake riƙe da shi na Jami’in Kula da Jarrabawa a sashen nasu.”