An kashe mutane aƙalla 85 a rikicin yankin tsakiyar Nijeriya – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sama da mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu a tsakiyar Nijeriya bayan da aka kashe mutane 85 a rikicin makiyaya da manoma, a cewar wani rahoto a ranar Alhamis.

Rikicin ya ɓarke ne a ranar Litinin da ta gabata, inda aka kashe mutane 30, a ƙauyuka da dama na Jihar Filato, yankin da ya kwashe shekaru yana fama da rikicin ƙabilanci da addini.

Rikicin dai ɗaya ne daga cikin ɗimbin ƙalubalen tsaro da ke fuskantar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, wanda zai karɓi ragamar mulkin ƙasar da ta fi yawan al’umma a Afirka a ƙarshen wannan watan.

Ba a dai san abin da ya jawo hare-haren na wannan makon a gundumar Mangu ba, amma kashe-kashen da aka yi tsakanin makiyaya da manoma yakan shiga kai hare-hare a ƙauyukan da wasu gungun ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka kai.

Joseph Gwankat, shugaban al’umma daga ƙungiyar ci gaban Mwaghavul na yankin, ya bayar da wannan adadin.

“Wani tawagar bincike da ceto sun gano gawarwaki 85,” kamar yadda ya shaida wa AFP.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta ce dubban mutane ne suka rasa matsugunansu tare da lalata ɗaruruwan gidaje sakamakon rikicin.

Fiye da gidaje 720 ko dai sun lalace ko kuma an lalata su gaba ɗaya.

Har yanzu ba a san adadin mutanen da suka jikkata ba har ya zuwa ranar Alhamis.

Gwankat, shugaban al’ummar ya bayyana cewa, mutane 57 da suka samu raunuka suna jinya a asibiti yayin da Nyelong na hukumar NEMA ya ce kimanin mutane 216 ne suka jikkata a hare-haren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *