An kashe yara yan shekara daya su shida a rikicin Kataf da Fulani.

A wani yunkuri mai kama da daukar fansa da wasu fusatattun samarin Katafawa suka kai wasu rugagen Fulani, a yanzu haka dai sun kashe wasu yara yan shekara 1 su shida da kuma wata mata.

Yaran da rikicin ya rutsa da su, sun hada da: Saidu Abdullahi, Mustapha Haruna, Sadiya da Zainab, sai kuma Aisha da Ya’u Kada.

Kwamishinan tsaro da al’amurran cikin gida na jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan ne ya shaida wa manema labarai, yadda abin ya faru.

“Hakan ta faru ne sanadiyar wani hari da wasu yan bindiga da ake zaton Fulani ne makiyaya suka kai wa al’ummar Katafawan a garin Gora gan, dake karamar hukumar Zangon Kataf a ranar Alhamis da ta gabata, inda aka hallaka mutane Bakwai, da wasu kuma da dama da suka samu raunuka.

Sai dai jami’an tsaro sun ce, an kashe wasu makiyayan su 7 a karamar hukumar Kauru ta jihar Kadunan.  Kuma a halin yanzu ana neman wasu mutim 5 da ba a san inda suke ba.

Rahoton ya kara da cewa, wasu mata su biyu da wasu maza biyu daga kabilun Fulani da suka samu raunuka a yanzu haka suna gaban likita ana kula da su.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*