An koka wa Gwamnan Bauchi kan yadda makaranta ta sukurkuce a Bogoro

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bogoro a Jihar Bauchi, Mista Ilya Habila ya koka matuƙa gaya da cewar, makarantar sakandare ta kwana guda ɗaya ƙwal da ke cikin ƙaramar hukuma ta sukurkuce raga-raga babu gyara.

Kamar yadda shugaban ya ce, illahirin gine-ginen da ke cikin makarantar da suka haɗa da gidajen malamai da ajujuwan da ake ɗaukar karatu kuma a koyar wa ciki, hatta dabbobi bai dace su kwana ciki ba.

Habila, yana jawabin marhabun ne a bikin fara rarraba kayayyakin tallafi na sana’o’i, dama bayar da jarin kuɗaɗe da na dabbobi kyauta ƙarƙashin shirin farfaɗo da komaɗar tattalin arzikin jama’a na Ƙauran Bauchi a ƙaramar hukumar ta Bogoro da kimanin mutane 1,000 za su amfana.

Ya ce, “Ya maigirma, wannan farfajiya da ake gudanar da wannan taro a yau, ita ce makarantar gwamnati guda ɗaya tak ta kwanan ɗalibai a cikin wannan ƙaramar hukuma, kuma ragargajewar ta wata manuniya ce ta rashin adalci muraran wa jama’ar wannan yanki da gwamnatocin baya suka yi.”

Habila ya ƙara da cewar, “Ɗaukacin makarantar tana bukatar yi mata kwaskwarima. In bacin ginin da yake ɗauke da ofisoshin gudanar wa na makarantar, kusan dukkan gine-gine dake cikin harabar makarantar babu ma daɗin kallo ballen tana shiga ga kowane mutum, hatta dabbobi bai kamata su kwana ciki ba.

“Amma muna da ƙwarin gwiwa lamura zasu canja a ƙarƙashin mulkin ka, kuma yaran mu za su ci gajiyar yin karatu a gwamnatin ka mai adalci”, Habila ya shaida wa gwamna.

Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ƙoƙarin son a kawo ɗauki wa hanyoyi da gonaki da ambaliyar ruwa ya lalata a cikin ƙaramar hukumar ta Bogoro a kwanakin baya.

Habila ya yi nuni da cewar, “Da ba don ɗauki da ka kawo mana ba, da hanyar da ake zirga-zirga akai zuwa garin Bogoro ta kasance gagarabadau, da ko wannan biki ba za a samu damar zuwa ba. Muna yi maka godiya bisa wannan ƙoƙari, mun gode.

“Shi ma babban asibiti dake garin Bogoro yana matuqar buqatar kwaskwarima, haɗi da wadata shi da kayayyakin gudanar da ayyuka na zamani. Ƙalubaloli nan ƙaramar hukuma suna da yawa, amma yanzu da ya kasance muna da gwamna, ba za mu voye su ba, za mu bayyana domin muna da yaqinin za a kula da su.”

A halin da ake ciki, Gwamna Bala Mohammed ya nuna kaɗuwarsa bisa cewar, duk da maqudan kuɗaɗe da gwamnatin sa ke kashewa domin gine-gine da gyare-gyaren makarantu da farfaɗo da lamuran ilimi baki ɗaya, har yanzu yara da suke ɗaukar karatu a gindin bishiya.

Gwamnan, akan hanyar sa ta shiga cikin garin Bogoro, kwatsam sai ya yi kiciɓis da yara suna ɗaukar darassuka a gindin wata bishiya da ke makarantar firamaren al’ummar garin Dajin da ke kan hanyar Dawaki zuwa Pankshin, inda ya yi tiris ya tsaya domin gane wa kansa wannan abun al’ajabi.

Gwamnan, a yayin da ya ya da zango a makarantar, ya yi jawabi wa malamai da ɗaliban makarantar, inda ya bayyana cewar, sam gwamnatin sa ba za ta yarda da irin wannan sakaci ba na rashin kayayyakin buƙatu a makarantun ta, la’akari da ƙoƙari da yake yi na bunƙasa sashin ilimi a jihar.

Don haka gwamna ya bayar da umarnin gaggawa wa ma’aikatar ilimi ta jiha data kawo ɗaukin gaggawa na gina ajujuwa a makarantar cikin makonni biyu.

Gwamna ya ce, “Ina matuƙar mamakin wannan hali duk da maƙudan kuɗaɗe da wannan gwamnati ke kashewa wa sashin ilimi, musamman wajen yi wa makarantu kwaskwarima da gina wasu sabbi, a ce har yanzu akwai yara da suka ɗaukar darassuka a gindin bishiyoyi a jihar Bauchi.”

Ya ce, “Sam, wannan ba  zata saɓu ba, gwamnatina ba za ta lamunci haka ba, a ce wasu yara a makarantun firamare suna ɗaukar darussuka a gindin bishiyoyi, sam ba zamu yarda da haka ba.”

Gwamna ya ce, “Bisa la’akari da wannan hali, ina umartar ma’aikatar ilimi ta jiha da ta gaggauta fara gina ajujuwan karatu a wannan makaranta cikin makonni biyu masu zuwa.”

Wani shugaban al’umma mai suna Bala Mai Hoto ya shaidawa gwamnan cewar, rashin abubuwan buƙatun koyarwa da ɗaukar karatu a makarantar yake kashe masu gwiwar tura yara zuwa makaranta.

Ya nuna matuƙar farin cikin sa da godiya wa Gwamna Bala Mohammed saboda tsayawa a wannan makaranta domin gane wa idanuwan sa yadda ake tafiyar da makarantu karkara.