An kuɓutar da basaraken da aka yi garkuwa da shi a Filato

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga Jihar Filato sun ce an kuɓutar da Sarkin Agwan Izere, Dr. Isaac Azi Waziri, wanda aka yi garkuwa da shi da sanyin safiyar Juma’a.

Blueprint ta rawaito maharan sun yi garkuwa da basaraken ne a fadarsa da ke gundumar Shere a shiyyar Jos ta Gabas.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da kuɓutar da Sarkin.

Haka nan, ya ce an cafke wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa ne da mutane a yankin.