An kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi

Daga CMG HAUSA

Alƙaluman da ma’aikatar aikin gona da raya ƙauyuka ta ƙasar Sin ta fitar sun nuna cewa, zuwa yanzu an kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi na lokacin kaka a ƙasar.

Yawan gonakin hatsi da aka girbe ya kai fiye da kadada miliyan 15.7, jimillar da ta kai kashi 18.1% na ɗaukacin gonakin hatsi dake ƙasar.

An bayyana cewa, yadda ake girbin hatsin cikin sauri, ya ƙaru da kaso 0.9, idan an kwatanta da na bara.

A dangane da yadda ake gudanar da aikin girbin hatsi a wurare daban daban na ƙasar kuwa, ya zuwa yanzu an riga an kammala rabin aikin girbi a yankin kudu maso yammacin ƙasar.

Yayin da a wuraren dake dab da kogin Yangtse, da kuma kudancin ƙasar, an girbe kaso 25 na hatsin da aka shuka.

A yayin da ake ƙoƙarin gudanar da aikin a sauran sassan ƙasar.

Haka zalika, ana hasashen cewa, za a yi amfani da na’urori da injunan aikin gona kimanin miliyan 30 a wannan lokacin kaka, don tabbatar da cewa, an gudanar da aikin girbin hatsi kamar yadda aka tsara.

Mai fassara: Bello Wang