An kwaɓe Nanono a damuna, an naɗa magajinsa a damuna

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Bara a damuna shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wani garambawul inda ya kwave wasu daga cikin ministocinsa da su ka haɗa da Tsohon Ministan Noma, Sabo Nanono da na Wutar Lantarki, Injiniya Saleh Mamman. Duk da tuni an naɗa magajin Mamman daga jihar Taraba wato ƙaramin ministan ayyuka Alhaji Mu’azu Sambo, amma sai bana a ka naɗa ministan da ya maye gurbin Sabo Nanono daga Kano wato Umar Yakub. Abin da ya ɗauki hankali na shi ne yadda lamarin ya dace da lokacin damuna.

Lokacin a ka cire Nanono har wani hoto a ka yaɗa a yanar gizo da ke nuna shi a gona inda a ka ce cikin raha gaskiya bai yi daɗi ba an kwave ministan noma a damuna, to ga shi yanzu kuma shuagaba Buhari ya sake naɗa magajin Nanonon a damuna. Ba lalle shugaba Buhari na duba lokaci ne wajen naɗa ministoci ko kwave su ba, amma wannan dace ya isa abun dubawa. Abin da ya fito fili a tsarin gwamnatin shugaba Buhari shi ne jinkiri wajen naɗawa ko sauke ministoci. Akwai lokacin da minista daga jihar Kogi Barista James Ocholi ya yi hatsarin mota kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda ya rasa ransa. A gaskiya an samu dogon lokaci kafin a naɗa magajinsa daga jihar Kogi.

In za a tuna lokacin akwai gurbin Amina Muhammed daga jihar Gombe da ta samu tafiya Majalisar Ɗinkin Duniya. Wani abu ma bayan naɗa Stephen Ocheni daga Kogi da Sulaiman Hassan, an samu akasin da ya jawo sai dogon lokaci kafin tantance su da tura su ma’aikatun da za su yi aiki. Gaskiya ni har ba zan yi mamaki ba idan har gwamnatin Buhari ta kammala ba tare da samun wanda za a naɗa ya maye gurbin Nanono ba. Ba mamaki don jihar Kano na da ministoci biyu ne a gwamnatin Buhari ya sa hankali ba zai koma kan rashin naɗa magajin Nanono ba. Janar Bashir Magashi ministan tsaro daga Kano kan ɗaukewa wasu kewar rashin maye gurbin Nanonon.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya naɗa sabbin ministoci 7 a gwamnatin sa don maye guraben da a ka samu a sanadiyyar kwaɓewa daga muƙami da kuma akasari da su ka yi murabus don takarar muƙamai a 2023. In za a tuna cikin waɗanda su ka yi murabus don neman takara akwai ministan Neja Delta Godswill Akpabio, ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu da ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Sanarwa naɗa sabbin ministocin na ƙunshe a wasiƙar da shugaban ya tura wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan don tantance ministocin kamar yadda tsarin mulkin Nijeriya ya tanada na shugaba ya canko waɗanda su ka kwanta ma sa a rai ya shigar da su gwamnatin sa inda ita kuma majalisar dattawa ta yi aikin tantancewa ta hanyar amincewa da naɗin ko ture naɗin da hakan zai sa shugaba ya sake zaɓo wani da zai turo don cin jarrabawar wannan naɗin.

Majalisar Dattawan za ta tantance sabbin ministocin a zaman da za ta yi na gaba don su samu shiga gwamnati da ta ke shekararta, ta ƙarshe kan karagar mulki. Kuma haƙiƙa ba wata fargabar majalisar za ta yi tutsu kan tantance mutanen 7 don yadda a ke da jituwa tsakanin gwamnatin ta Buhari da shugabannin majalisar. Ba ma mamaki in an duba yadda ma tun farko shugabannin su ka zo da samun mara bayan fadar Aso Rock ba kamar yadda ya faru a majalisar da ta gabata ba zamanin Bukola Saraki.

Sabbin ministocin sun haɗa da Henry Ikechukwu daga jihar Abia, Umana Umana daga Akwa Ibom, Ekuma Joseph daga jihar Ebonyi, Goodluck Obia daga Imo, Umar Yakub daga Kano, Ademola Adegorioye daga jihar Ondo da Odo Udi daga jihar Ribas. Ba a san shin ko waɗanda a ka cankar na da jituwa da waɗanda a ka sauke in ka ɗebe na Nanono ko kuwa a’a. Don alamu na nuna hatta ministocin da su ka yi murabus ka iya zama in da sun fasa takarar har zuwa ƙarshen gwamnatin shugaba Buhari. Misali mafi tasiri shi ne akwai ministoci da dama da su ka samu shiga gwamnatin Buhari tun watan Oktoba na shekara ta 2015 kuma har yau da su a ke damawa a gwamnatin

A zahiri wannan sauyi bai shafi wasu ministocin da su ka nuna niyyar takara amma daga bisani su ka janye ba kamar ministan shari’a Abubakar Malami daga Kebbi da Chris Ngige daga jihar Anambra. Ministocin da su yi ribas na nan daram a gwamnatin duk da an tabbata ba su so janye takara ba. Muradin waɗannan ministocin shi ne su samu yin takara alhali su na kan kujerun su. Wannan lamarin har kotu ya kai inda daga bisani shugaba Buhari ya umurci duk mai niyyar takara daga cikin masu mukaman gwamnatinsa ya yi murabus zuwa wata ranar litinin. Hakan kuwa a ka yi wasu su ka yi murabus wasu su ka yi ribas.

Wannan mataki ya rage muhawarar wasu ministocin na son amfani da ƙarfin kujerar gwamnati wajen cimma muradunsu na siyasa. Ba ma sai an faɗa ba umurnin na shugaba Buhari ya bayar ya zo wa wasu ministocin da bazata don a yanayin shugaban mai jimirin gaske kan ɗabi’un jami’ansa, zai zama da mamaki in ya ɗauki wannan muqami na ba sani ba sabo.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce, ba shi kaɗai ke da hurumin kwave gwamnan babban banki Godwin Emefiele ba duk da shi ya naɗa shi.

Shugaban na maida amsa ne kan tambaya daga kafar labarun Bloomberg kan dalilan gaza kwaɓe gwamnan duk da ya ayyana qudurin shiga siyasa har ma ga takarar shugaban ƙasa. In za a tuna da farko Emefiele ya musanta batun takarar amma sai a ka ga magoya bayan san a annashuwa da daga hotunansa a babban taron zaɓen sabbin shugabannin APC. Bayan nan kuma a ka bi tsawon titin da ya ratsa gaban babban bankin an manne shi da hotunan Emefiele ba tare da an ga wani ya zo ya yaga ba. Wani abu har kotu gwamnan ya garzaya ya na mai buqatar ta ba shi dama a ƙarƙashin doka ya yi takararsa alhali ya na kan kujerar kula da kuɗin Nijeriya.

Shugaba Buhari ya ce shi ke da ikon naɗa gwamnan amma majalisar dattawa ke da hurumin tantance shi. Sai dai a nan shugaban bai ce majalisar na da hurumin kwave gwamnan ba ko kuwa a ce shi kan bai ce in har zai kwave gwamnan sai ya miƙa wasiƙa ga majalisar ba kasancewar akwai wa’adin da gwamnan ke yi kan gado kafin naɗa sabo.

Hakanan shugaban ya ce majalisar gudanarwa ta babban bankin ne za ta zauna ta duba ko matakan na Emefiele sun hana shi gudanar da aikinsa na jagorantar babban bankin. Tambaya a nan ko ita ma majalisar babban bankin na da hurumin dakatar da gwamnan in ta same shi da laifi?.

Muhawara kan neman takarar Emefiele ta ƙara zafi ne bayan hukumar zaɓe INEC ta ce ba za ta amince da ajiye muhimman takardun zave a babban bankin ba don gwamnan babban banki ya nuna ɓangarensa a siyasa maimakon ya zama ɗan ba ruwan mu.

Emefiele dai wanda tsohon shugaba Jonathan ya naɗa bayan kwabe Sunusi Lamido Sunusi, ya samu nasarar shugaba Buhari ya sabunta ma sa wa’adin mulki don alamun gamsuwa ga aikin da ya ke gudanarwa. Emefiele zai sauka daga muƙamin ne bayan ma gwamnatin Buhari ta sauka da shekara ɗaya wato an ma sa sabon wa’adin shekaru 5 a watan mayun 2019.

A na zargin Emefiele da cewa wasu masu faɗa a ji a gwamnatin Buhari su ka ɗaure ma sa baya ya ke ta wanzuwa kan wannan babban mukami don da zargin da a ka yi ma sa na amincewa da fidda kuɗi a zamanin tsohuwar gwamnati ko da a umurni kan takardar tsire ne.

Kammalawa:

Ko ba a ce komai ba za a fahimci ministoci a gwamnatin shugaba Buhari na zama ’yan lele don damar da su ke samu daga shugaban da ba ya tsangwama ga waɗanda ya naɗa mukamai matuƙar ba wani babban ƙorafi a ka kai kan teburinsa ba. Gaskiya dai ɗaya ce waɗannan ministocin na gudanar da aikinsu ba tare da katsalandan ba. Wasu sun cimma ’yan ayyukan da za su iya ba da labari wasu kuma kamar ba su fahimci ainihin abin da ya dace su aiwatar a ma’aikatun da a ka tura su ba. Rashin dubawa da la’akari da ƙwarewar ministan da tarihin aikinsa kafin tura shi ma’aikata kan yi tasiri wajen taɓuka abun kirki ko akasin haka a lokacin da ya shiga ofis. Kazalika idan ma an tura minister ma’aikata ya lura linzami ya fi bakin zakara sai ya nemi wasu ƙwararru da ya amince da su, su zagaye shi su na dora shi kan hanya kan cimma nasara. Hakan fa ga mai son cimma nasarar tallafawa ayyukan raya ƙasa ne ba raya aljihu ba. Yo ai ko mutum ba shi da basirar aiki zai san yadda zai raya aljihunsa ba tare da buƙatar taimakon na waje da fage ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *