An mayar da Hukumar Rijistar ’Yan Ƙasa ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alamu na nuna cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta mayar da Hukumar Kula da Rijistar ’Yan Ƙasa (NIMC) daga Ma’aikatar Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani ta Tarayya zuwa Ma’aikatar Kula Da Harkokin Cikin Gida ta Tarayya.

Majiyoyi a cikin Hukumar NIMC, waɗanda suka tabbatar da hakan ga manema labarai, sun ce, ko da yake ba a bayyana shi a hukumance ba, amma za a fitar da sanarwar a nan gaba.

An tattaro cewa matakin mayar da hukumar zuwa ma’aikatar harkokin cikin gida shi ne don magance matsalolin da ke da nasaba da bayar da Lambobin Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN), wanda shi ne babban abin da ake buƙata na neman da kuma karvar fasfo ɗin Nijeriya.

Idan za a iya tunawa, a watan Agusta 2020, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da miqa hukumar NIMC zuwa ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin dijital ta tarayya.

Sai kuma Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Farfesa Isa Pantami, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce amincewar miqa ayyukan ya ta’allaka ne kan la’akarin da shugaban ƙasa ya yi kan muhimmiyar rawar da NIMC ke takawa wajen cimma manufofin tattalin arziki na dijital na ƙasa (NDEPS).

A halin da ake ciki, NIMC ta bayar da NIN miliyan 102.4 ga ‘yan Nijeriya kamar yadda aka faɗa a watan Agusta.

A cikin sabbin bayanai, bugu na Agusta, alƙaluma sun nuna cewa Legas ce ke kan gaba inda mazauna miliyan 11.17 suka yi rajistan NIN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *