An naɗa ƴar Shugaba Tinubu Jakadar Hukumar Kula da Almajirai

Daga BELLO A. BABAJI

An naɗa ƴar Shugaba Bola Tinubu, Folasade Tinubu-Ojo a matsayin Jakadar Hukumar Kula Almajirai da Ilimin Yaran da ba sa zuwa Makaranta.

Babban Sakataren hukumar, Muhammad Sani Idris ya faɗi hakan a yayin wata ziyara da ya kai gidan Tinubu-Ojo da ke Legas.

Cikin sanarwar da ya fitar, Sakataren ya ce ƙoƙarin da Tinubu-Ojo ke yi na inganta rayukan al’umma a garuruwa musamman Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ya taimaka wajen bata muƙamin.

Ya kuma yaba wa ƙoƙarinta ga harkokin kasuwanci musamman a ɓangare inganta mata da kiraye-kirayen a tallafa musu.

A lokacin da ta ke jawabi, Tinubu-Ojo ta yi godiya ga karrama ta da aka yi na bata muƙamin, ta na mai jaddada cigaba da yaƙin neman samar wa yara a Nijeriya ingantacciyar rayuwa.