An naɗa Baba a matsayin muƙaddashin IGP

Daga UMAR M. GOMBE

A halin da ake ciki, Alkali Baba ya zama muƙaddashin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya. (IGP).

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci bikin naɗa sabon muƙaddashin a ranar Laraba kuma a Fadar Shugaban Ƙasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Wa’adin Mohammed Adamu a matsayin shugaban rundunar ya ƙare ne a Fabrairun da ya gabata bayan da ya cika shekara 35 da aiki. Inda daga bisani Shugaba Buhari ya ƙara masa watanni uku.

Waɗanda suka halarci bikin naɗin har da tsohon IGP Mohammed Adamu; Sakataren Gwamnantin Tarayya (SGF); Boss Mustapha; Ministan Harkokin ‘Yansanda, Maigari Dingyadi, Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu da kuma takwaransa na ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Laolu Akande da sauransu.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan naɗin nasa, Alkali Baba ya sha alwashin yin aiki tukuru don inganta aikin ɗansanda.

Haka nan ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su bai wa ‘yansanda haɗin kai wajen gudanar da harkokinsu domin samun nasarar dawo da tsaro yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *