An naɗa Ibrahim Garba Shuaibu sabon Sakataren Yaɗa Labaran Mataimakin Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin Sakataren Yaɗa Labaran Mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Juma’a.

Shuaibu ya yi karatun digirinsa na farko a jami’ar Bayero Kano, inda ya karanci Laburari, inda kuma yanzu haka yake digiri na biyu a kan ‘PR’. kuma shi ne wakilin.

Kafin naɗin nasa, shi ne Shugaban ƙungiyar ƴan jaridu masu aikewa da rahotanni daga Jihar Kano.

kuma shi ne Shugaban kamfanin Jaridar yanar Gizo ta Prime Time News.

Kazalika, Gwamnan Abba Kabir Yusif ya amince da naɗin wasu mutane shida domin zama hadimai na musamman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *