An naɗa Malagi Darakta a kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC

Daga WAKILINMU

An naɗa mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris (Malagi), a matsayin Daraktan Sadarwa na Kwamitin Shugaban Ƙasa (PCC) na Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Shettima ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Sakataren Kwamitin, Rt. Hon. James Abiodun Faleke, wanda jami’yyar ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kwamitin mai mambobi 422, na gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin mataimakinsa.

An zaɓi Alhaji Mohammed Idris Malagi, tsohon ɗan takarar gwamnan APC a jihar Neja, a wannan matsayi ne bisa la’akari da ƙwarewarsa a fannoni daban-daban musamman kuma a fannin yaɗa labarai.

Sai kuma la’akari da yadda ya ba da gudunmawarsa mara misaltuwa ga Jam’iyyar APC a matakai daban-daban.

Malagi, shi ne shugaban kamfanin buga jarida na Blueprint Newspapers Limited, wanda ke wallafa jaridun Manhaja da Blueprint Daily da Blueprint Weekend, kuma shugaban Gidan Rediyon We FM.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *