An naɗa Shugaban Ƙasa na riƙon-ƙwarya a Iran

Jigon ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya naɗa Mataimakin Shugaban Ƙasar, Mohammad Mokhber, a matsayin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙasar biyo bayan mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi, wanda ya cimma ajali a hatsarin jirgin sama.

An jiwo jigon na cewa, “Bisa la’akari da Doka ta 131 ta kundin tsarin mulkin ƙasar, yanzu Mokhber shi ne jagoran ɓangaren zartarwa.”

Khamenei ya bayyana haka ne a sanarwar da ya fitar, inda ya ce Mokhber na buƙatar yin aiki tare da shugabannin ɓangaren doka da shari’a domin shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa a cikin wa’adin kwana 50.