An naɗa wa ɗan jarida, Ɗahiru Maihula, sarautar Kacallan Kutunbawa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai unguwar Kutumbawa a jihar Kano, Alhaji Mustapha Abubakar Rimin Kira ya  naɗa ɗan jarida Dahiru Muhammad Maihula a matsayin Kacallan Kutumbawa da ya gudana a Unguwar Rimin Kira, Kano.

Dahiru Maihula dai shi ne  Darakta a kamfanin yaɗa labarai da ke Kano, wato DMM.

Tarihi ya nuna cewa Kano ta yi sarakuna da dama  daga zuri’ar Kutumbawa da suka haɗa da: Muhammadu Alwali Kutumbi 1623-1643 da Alhaji Ɗan Kutumbi 1648-1649 da Shekarau (ll) 1649-1651 da Muhammadu Kukuna.1651-1652 da Sarki Soyaki (ya yi sarki sau biyu,1652) da Sarki Bawa 1660-1670 da Sarki Dadi a 1670-1703 da Muhammad Sharif 1703-1731.

Sauran sun haɗa da: Sarki Kumbari a 1731-1743 da Al-Hajj Kabe a 1743-1753 da Sarki Yaji (ll) a 1753-1768 da Baba Zaki a 1768-1776 da Dauda Abasama (ll) 1776 -1781 da kuma Muhammad Alwali a 1781-1805.

Da ya ke ƙarin haske mai unguwar Kutumbawa ya ce duba da yadda Dahiru Maihula ya ke jajirtacce kuma haziƙi ya sa ya naɗa shi domin ƙarfafa gwiwa da irin ƙoƙarin da ya ke yi,

Masana tarihi na ra’ayin cewa wanda ya yi sarkin Kano, kafin jihadin Sheikh Usman Bin Fodio, wato Aliyu Yaji, ɗan zuri’ar Kutumbawa ne wanda ya yi aiki tuƙuru wajen yaɗa addinin Musulunci a Kano.

Kazalika, Sarki Aliyu Yaji ya yaqi al’adar nan ta mutan Kano a wancan lokaci, wato “Dirki”
‘Dirki’ katafaren wuri ne kusa da Babban Masallacin Kano inda jama’ar Kano a wancan lokaci kan kai fatu su jibgi bayan yanka dabbobi yayin Babbar Sallah.

A wancan lokaci jama’a sun mayar da ‘Dirki’ wajen bauta na musamman inda suka yi amannar cewa wuri ne na karɓar addu’o’insu.
Taron naɗin dai ya samu halartar manya manyan sarakuna, yan kasuwa, ‘yan jarida da kuma ‘yan uwa da abokan arziƙi.